ha_tn/3jn/01/01.md

1.4 KiB

Mahaɗin Zance:

Wannan wasiƙa ce daga Yahaya zuwa ga Gayus. Dukan inda aka mori "ka" ana nufin Gayus ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-you)

dattijon

Wannan ya na nufin Yahaya, manzo da kuma almajirin Yesu. Watakila ya kira kansa "dattijo" saboda shekarunsa ko kuma domin shi shugaba ne a ikillisiya. Ana iya sa sunan marubucin a bayyane. "Ni, Yahaya dattijo, ina rubutu." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Gayus

Wannan ɗan'uwa mai bi ne wadda Yahaya ya rubuto masa wannan wasiƙan. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

wanda nake ƙauna da gaske

"wadda na ke ƙauna ta gaskiya"

domin ka samu albarka cikin kowanne al'amari, da kuma ƙoshin lafiya

"ku kasance da nasara cikin kowanne al'amari, ka kuma kasance da ƙoshin lafiya"

kamar yadda ruhun ka yake lafiya

"kamar yadda kake lafiya a ruha"

'yan'uwa suka zo

"yan'uwa masubi sun zo." Da alama waɗannan mutanen maza ne duka.

ka yi tafiya cikin gaskiya

Tafiya a hanya, na nufin yadda mutum yake rayuwarsa. AT: "Ku na rayuwar ku a bisa gaskiyar Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

'ya'yana

Yahaya yana magana game da wadda ya koyar da su game da bangaskiya cikin Yesu kamar su 'ya'yansa ne. Wannan ya na nanata ƙaunarsa garesu da kulawa da yake da shi dominsu. Yana kuma iya zama cewa shi ne ya kai su ga sanin Ubangiji. AT: " 'ya'yana na ruhu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)