ha_tn/2ti/01/01.md

1.8 KiB

Muhimmin Bayani:

A wannan littafin, kalmar nan "mu" na nufin Bulus ne da Timoti, sai inda aka ce ba haka ba, (Timoti shine wanda aka rubutawa wannan wasiƙa) da kuma dukan masubi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

Bulus ...zuwa Timoti

Mai yiwuwa harshen ku na da yadda ake gabatar da marubucin wasiƙa; yi amfani da shi. Haka kuma bayan gabatar da marubucin yana iya yiwuwa a ga bukatar gabatar da wanda ake rubuta wa wasiƙan.

ta wurin nufin Allah

"saboda nufin Allah" ko "domin Allah ya so haka." Bulus ya zama manzo domin haka Allah ya so ba domin zaɓen mutum ba.

bisa ga

Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "domin manufar." Wannan na nufin cewa Allah ya zaɓi Bulus domin ya faɗa wa mutane game da alkawarin Allah na samun rai cikin Yesu, ko 2) "bisa dalilin." Wannan na nufin cewa kamar yadda Allah yayi alkawarin rai ta wurin Yesu, haka nan ya mayar da Bulus ya zama manzo.

na rai da ke a cikin Almasihu Yesu

Bulus na magana game da "rai" kamar wani abu ne da ake samu a cikin Yesu. Wannan na bayyana rai da mutane ke samu ta wurin zama na Almasihu Yesu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ƙaunataccen ɗa

"ɗa da nake so" ko "ɗan da nake ƙauna. Anan "ɗa" kalma ce na ƙauna mai muma girma da amincewa. Mai yiwuwa ta hannun Bulus ne Timoti ya karɓi Almasihu, shiyasa Bulus ya dauke shi a matsayin ɗansa. AT: "wanda ya ke a matsayin ƙaunataccen ɗa na" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Alheri, jinkai, da salama daga

"Bari alheri, jinkai, da salama sukasance a gare" ko "Bari ku kasance da alheri, jinkai, da salama a cikin ku daga"

Allah Uba da

"Allah, wanda shine Ubanmu, da." Wannan muhimmin suna ne na Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)

Almasihu Yesu Ubangijimu

"Almasihu Yesu, wanda shine Ubangijimu"