ha_tn/2sa/22/05.md

1.0 KiB

Muhimmin Bayani:

Waƙar Dauda ga Yahweh ta ci gaba. Yana amfani da kwatankwacinsa don ƙarfafa abin da yake faɗa. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)

Gama ambaliyun mutuwa sun kewaye ni, haukan ruwayen hallakarwa sun tsoratadda ni

Dauda ya kamanta miyagun mutanen da suke so su kashe shi da ambaliyar ruwa da ke shirin nutsar da shi. Waɗannan jimlolin suna da ma'anoni iri ɗaya kuma ana amfani dasu don ƙarfafawa. (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]])

haukan ruwayen hallakarwa sun tsoratadda ni

Wannan hoto ne na ambaliyar ruwa da ke tafe da sauri wanda ke lalata komai a cikin hanyar su.

Igiyoyin lahira sun kewaye ni; tarkunan mutuwa sun kama ni

Dauda yayi magana akan mutuwa da Lahira kamar mutane ne waɗanda suke ƙoƙari su kama shi kamar yadda maharbi yake kama dabbobin. Waɗannan jimlolin suna da ma'anoni iri ɗaya kuma ana amfani dasu don ƙarfafawa. (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-personification]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]])