ha_tn/2sa/19/34.md

1.7 KiB

"Sauran kwanaki nawa suka rage cikin shekarun rayuwata, da zan haura tare da sarki zuwa Yerusalem?

Anan Barzillai yana nufin ya tsufa kuma babu wani dalili da zai sa shi ya bi Dauda. Ana iya fassara wannan tambayar a matsayin sanarwa. AT: "Tabbas ba zan rayu ba shekaru da yawa. Babu wani kyakkyawan dalili da zai sa in tafi tare da sarki zuwa Yerusalem." (Duba: fgis_rquestion)

Zan iya banbance tsakanin abu mai kyau da mugu?

Barzillai yayi amfani da tambayoyi don jaddada dalilin da yasa baya son zuwa Yerusalem. Anan "mai kyau" da "mara kyau" suna nufin abin da yake kyawawa da wanda kyawawa ba. Ana iya rubuta wannan tambayar azaman sanarwa. AT: "Ba zan iya bambance tsakanin abin da yake kyawawa da wanda kyawawa ba." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Ko bawanka zai iya ɗanɗana abin da nake ci ko abin da nake sha?

Barzillai yayi amfani da tambayoyi don jaddada dalilin da yasa baya son zuwa Yerusalem. Ana iya rubuta wannan tambayar azaman sanarwa. AT: "Ba zan iya jin daɗin ɗanɗanar abin da nake ci da abin da nake sha ba." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Donme bawanka za ya zama nawaya ga shugabana sarki?

Barzillai ya yi amfani da wannan tambayar don jaddada cewa ba ya son ya zama nauyi ga sarki. Ana iya rubuta wannan azaman bayani. AT: "Kada bawanka ya tafi tare da kai ya zama maka nauyi." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Donme sarki zai saka mani da irin wannan ladar

Barzillai ya yi amfani da wannan tambaya don jaddada cewa bai san dalilin da yasa sarki zai saka masa da wannan hanyar ba. Ana iya rubuta wannan azaman bayani. AT: "Ban san dalilin da yasa sarki zai saka min da wannan lada mai girma ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)