ha_tn/2sa/18/01.md

1.2 KiB

Dauda ya ƙidaya sojojin da ke tare da shi

Dauda bai ƙidaya mutanen duka ba, amma waɗansu mutane suka ƙidaya. AT: "Dauda ya yi umarni don a ƙidaya sojojin da suke tare da shi kuma ya sanya" ko "Dauda ya tsara sojojin da suke tare da shi kuma ya naɗa su" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

naɗa shugabanni na dubbai da na ɗarurruka a bisansu

Mai yiwuwa ma'anoni su ne 1) waɗannan lambobin suna wakiltar ainihin adadin sojojin da waɗannan kaftin ɗin suka jagoranta. AT: "shugabannin sojoji 1,000 da shugabannin sojoji 100" ko kuma 2) kalmomin da aka fassara a matsayin "dubbai" da "ɗaruruwan" ba sa wakiltar ainihin lambobi, amma sunaye ne na manya da ƙananan ƙungiyoyin soja. AT: "shugabannin sojoji na manyan rundunonin soja da shugabannin kananan rundunonin sojoji" (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-numbers)

shugabanni

Kyaftin mutum ne wanda yake da iko akan ƙungiyar sojoji.

Lallai zan fita tare daku da kaina, nima

Wannan yana nufin cewa zai fita tare da su zuwa yaƙi. Ana iya bayyana wannan a sarari. AT: "Ni da kaina zan tafi tare da ku zuwa yaƙi" ko "Ni da kaina zan tafi tare da ku zuwa yaƙi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)