ha_tn/2sa/16/22.md

1.1 KiB

Absalom kuwa ya kwana da mata bayin mahaifinsa a idanun dukkan Isra'ila

Wannan yana nufin cewa mutane suna iya ganin rumfar kuma Absalom yana tafiya yana fita daga cikin rumfar tare da matan. Maganar "duk Isra'ila" ta zama gama gari, don kawai mutanen da ke kusa da gidan sarauta ne za su iya ganin ta. AT: "inda Isra'ilawa zasu ganshi ya shiga rumfar" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-hyperbole)

Ya zama kuwa shawarar da Ahitofel ya bayar a waɗannan kwanaki ta zama kamar wadda mutum ya ji

A nan marubucin ya kwatanta yadda mutane suka amince da shawarar Ahitofel da yadda za su amince da shawara kai tsaye daga Allah. AT: "Yanzu mutane sun aminta da shawarar Ahitofel a waccan zamanin kamar yadda za su amince da shi idan ya zo" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

mutum ya ji daga bakin Allah da kansa

A nan bakin Allah yana wakiltar kansa kuma yana ƙarfafa jawabinsa. AT: "kamar dai Allah ne ya faɗi hakan da bakinsa" ko "kamar dai mutum ya ji maganarsa da kansa Allah" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-rpronouns]])