ha_tn/2sa/12/21.md

950 B

Muhimmin Bayani:

Waɗannan ayoyin suna ƙunshe da tambayoyin magana waɗanda ke jaddada cewa Dauda ya gane cewa Yahweh ya bar wannan ya faru.

Wa ya sani watakila Yahweh zai yi mani alheri, ya bar yaron da rai?

Dauda ya yi wannan tambayar don tausayawa cewa babu wanda ya san ko Yahweh zai bar yaron ya rayu. Ana iya fassara wannan tambaya a matsayin sanarwa. AT: "Ba wanda ya san ko Yahweh zai yi mani alheri ko a'a don yaron ya rayu." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Amma yanzu ya mutu, to donme zan yi azumi?

Dauda ya yi wannan tambayadon jin tausayin cewa ba shi da dalilin yin azumi. Ana iya rubuta wannan azaman bayani. AT: "Yanzu da ya mutu ba zai da wani amfani ba yin azumin ba kuma." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Ni zan je gunsa

Dauda yana nuna cewa zai je inda ɗansa yake idan ya mutu. AT: "Lokacin da na mutu zan je inda yake" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)