ha_tn/2pe/02/12.md

2.2 KiB

waɗannan dabbobi marasa tunani an yi su ne musamman domin a kama a kuma hallaka su

Daidai kamar yadda dabbobi ba su da tunani, waɗannan mutane ba za a iya muhawara da su ba. AT: "waɗannan masu koyaswar karya suna kamar dabbobin da ba sa tunani wanda aka kama su domin hallaka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ba su san abin da suna zargi ba

Suna miyagun maganganu game da abin da ba su sani ko fahimta ba.

Za a halaka su

AT: "Allah zai halaka su" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Za su karɓi sakamakon muyagun ayyukansu

Bitrus yana magana game da hukuncin da masu koyaswar ƙarya za su samu kamar wata sakamako ne. AT: "Za su karɓi abinda ya cancance su saboda miyagun ayyukansu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-irony)

nishaɗi da rana

A nan kalmar nan "nishaɗi" na nufin ɗabi'u marasa kyau duk da handama, shaye- shaye da kuma haramtattun ayyuka. Yin waɗannan abubuwan da rana na nuna cewa waɗannan mutane ba sa kunyan wannan hali.

datti ne da lahani gare su

Kalmomin nan "datti" da "lahani" suna da ma'ana kusan iri ɗaya. Bitrus ya yi magana game da malaman karya sai ka ce su datti ne a tufa, wadda ke sa kunya ga waɗanda suka sa ta. AT: "Su kamar datti ne da kuma lahani a kan tufafi, wadda ke sa kunya" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-doublet]])

Idanun su cike suke da sha'awace-sha'awacen zina

A nan "idanu" na nufin sha'awace-sha'awace kuma "idanu cike" na nufin cewa sun cika son abu. AT: "Koda yaushe su na son aikata zina" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

ba sa taɓa gamsuwa da zunubi

Kodashike sun yi zunubi don su samu gamsuwa cikin sha'awar su, zunubin da suka yi bai taɓa gamshe su ba.

Suna rinjayar waɗanda ba su da tsayayyan a ran su

A nan kalman nan "ran" na nufin mutanen. AT: "Sun rinjayi mutanen da ba sa tsayawa a guri ɗaya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

kafa zukatansu ga haɗama

A nan kalmar nan "zukata" na nufin tunani da shauƙin mutumin. Saboda halayen da suka saba yi, sun hori kansu ga yin tunani da kuma yin ayyuka bisa ga haɗama. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)