ha_tn/2pe/02/10.md

1.3 KiB

Wannan kuwa gaskiya ne na musamman

Kalmar nan "wannan" na nufin cewa Allah ya sa mutane marasa Adalci cikin kurkuku har ya zuwa ranar shari'a bisa ga 2 Peter 2:9.

waɗanda suka cigaba cikin mugayen sha'awace-sha'awace na jiki

A nan "sha'awace sha'awace na jiki" na nufin sha'awace-sha'awace ta halin zunubi na mutuntaka. AT: "waɗanda sun cigaba da dulmuya cikin sha'awace-sha'awace ta zunubi"

raina mulki

"sun ƙi biyayya da mulkin Allah." Anan kalmar nan "mulki" mai yiwuwa na nufin ikon Allah.

mulki

A nan "mulki" na a madaddin Allah wanda ke da ikon bada umurni da kuma hukunta rashin biyayya. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

yin ganin dama

"aikata kowane abinda suke so su yi"

masu ɗaukaka

Wannan na nufin halitattun ruhohi kamar mala'iku ko kuwa aljannu.

ƙarfi da iko ƙwarai

"ƙarfi da iko fiye da masu koyarwar ƙarya"

amma basu kawo karar ɓatancin găbă da su ba

Kalman nan "su" na nufin mala'iku. Ma'anoni masu yiwuwa na kalmar nan "su" na kamar haka 1) masu ɗaukaka ko kuwa 2) masu koyarwar ƙarya.

kawo karar ɓatanci găbă da su ba

Ra'ayin cewa mala'iku na iya zargin waɗannan mugayen mutane na kamar za su iya kai masu hari ta wurin amfani da zargi a matsayin makamai. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)