ha_tn/2pe/02/04.md

1.7 KiB

Mahaɗin Zance:

Bitrus yana bada misalan mutanen da ke gãbã da Allah da kuma wanda Allah ya hukunta saboda abinda suka yi.

bai rangwata

"bai dena hukunci" ko "ya hukunta"

ya mika su zuwa ga baƙin duhu ta jahannama

Kalmomin nan "bakin duhu ta jahannama" kalmomi ne a addinin Helenawa dake nufin wurin da aka hukunta mugayen ruhohi da kuma mugayen mutanen da suka mutu. AT: "ya jefa su cikin jahannama" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

a baƙin duhu cikin sarƙoƙi

AT: "inda zai sa su cikin sarƙar baƙin duhu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

cikin sarkokin baƙin duhu

Wannan na iya nufin 1) "a sarƙa cikin wurin da ke da matuƙar duhu" ko kuwa 2) "cikin matuƙar duhun da ta sa su cikin kurkuku kamar sarƙoƙi." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

har ya zuwa ranar hukunci

Wannan na nufin ranar shari'a a sa'ad da Allah zai shar'anta kowane mutum.

bai rangwata wa duniya ta dã ba

A nan kalman nan "duniya" na nufin mutanen da ke cikin ta. AT: "bai rangwata wa mutane da sun yi rayuwa cikin duniya ta dã ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

ya keɓe Nuhu ... da wasu guda bakwai

Allah bai halaka Nuhu da mutane bakwai ba a sa'ad da ya halaka sauran mutane wanda sun yi rayuwa a duniya ta dã.

ƙona biranen Saduma da Gwamrata da wuta ya maishe su toka

"kona biranen Saduma da Gwamrata da wuta har suka zama toka"

yi mu su hukuncin halaka

A nan kalman "su" na nufin Saduma da Gwamrata da kuma mutanen da sun yi rayuwa cikin su.

maishe su abin misalin abin da zata faru da marasa bin Allah

Saduma da Gwamrata sun zama misalai ne da kuma kashedi na abin da zai faru da waɗanda sun yi wa Allah rashin biyayya.