ha_tn/2pe/02/01.md

1.6 KiB

Muhimmin Bayani:

Bitrus ya fara yi wa masubi kashedi game da masu koyarwar ƙarya.

Annabawan ƙarya sun zo wurin mutane, kuma masu koyarwar ƙarya za su zo wurin ku kuma

Kamar yadda masu koyarwar ƙarya sun zo suna yauɗaran Isra'ila da kalmomin su, haka kuma masu koyarwar ƙarya za su zo suna koyarwar da karya game da Almasihu.

karkatacciyar koyarwa mai hallakaswa

kalmomin nan "karkatacciyar koyarwa" na nufi ra'ayoyin da ke dabam da koyarwar Almasihu da kuma manzannni. Wannan karkatacciyar koyarwar na rushe bangaskiyar wanɗanda suka gaskanta da ita.

ubangidan da ya saye su

Kalman "ubangidan" a nan na nufin mutumin da ke da bayi. Bitrus yana magana game da Yesu a matsayin mamallakin mutane da ya saya, mutuwarsa ita ce farashin. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]])

son sha'awa

haramtaccen hali ta jima'i

za a yi saɓo ga hanyar gaskiya

Maganan nan "hanyar gaskiya" na nufin bangaskiyar masubi a matsayin hanya ta gaskiya zuwa ga Allah. AT: "marasa bi za su yi saɓo ga hanyar gaskiya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

ribance ku ta wurin maganganunsu na yauɗara

"shawo kan ku ga bada kuɗi ta wurin yi muku karya"

Hallakarsu ba za ta yi jinkiri ba; hukuncinsu na nan tafe

Bitrus yana magana game da "hallaka" da "hukunci" sai ka ce su mutane ne da za su iya yin abu. Maganganun nan biyu a takaice abu ɗaya ne su na nanata yadda masu koyarwar karya za su hallaka jim kaɗan. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-personification]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]])