ha_tn/2ki/15/29.md

1.8 KiB

A kwanakin Feka sarkin Isra'ila

Ana iya bayyana hakan a sarari da cewa ana nufin kwanakin mulkin Feka. AT: " A kwanakin mulkin Feka sarkin Isra'ila" ko "A wancan lokacinda Feka ya zama sarki a Isra'ila. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Tiglat Filesa

A cikin 2 Sarakuna 15:19 an kira wannan mutumin "Ful." (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

Ijon ... Abel Bet Ma'aka ... Janoya ... Kedesh ... Hazor ... Giliyad ... Galili ... Naftali

Waɗannan su ne sunayen biranen ko yankuna. (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

Ya ɗauki mutanen zuwa Asiriya

Anan "ya" yana nufin Tiglat Filesa kuma yana wakilta shi da rundunarsa. Caraukar mutane zuwa Asiriya alama ce ta tilasta musu su tafi Asiriya. AT: "Shi da rundunarsa sun tilasta mutane su tafi Asiriya (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

mutanen

Ana iya bayyanawa a fili waɗanne irin mutane ne waɗannan. Watau fassarar: "mutanen waɗancan wuraren" ko "jama'ar Isra'ila" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Hosheya ... Elah

Waɗannan sunayen mutane ne. (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

Ya kai masa hari ya kuma kashe shi

"Hosheya kuwa ya kai wa Feka hari, ya kashe shi"

a shekara ta ashirn ta Yotam ɗan Uziya

Ana iya bayyanawa sarai cewa wannan shekara ce ta ashirin ta sarautarsa. AT: "A shekara ta 20 ta mulkin Yotam ɗan Uziya" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]] da [[rc:///ta/man/translate/translate-numbers]])

a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai aiki. AT: "Kuna iya karanta game da su a littafin al'amuran sarakunan Isra'ila" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)