ha_tn/2jn/01/12.md

746 B

ban so in rubuta su da alƙalami, tawada da kuma takarda ba

Yahaya bai so ya rubuta sauran waɗannan abubuwan ba, amma zai so ya zo ya faɗa masu. Bai faɗa masu cewa zai rubuta masu da wani abu dabam da alƙalami, tawada da kuma takarda ba.

magana fuska da fuska

"Fuska da fuska" a nan na nufin yin magana a gabansu. AT: "yi magana a gabanku" ko "yi magana da ku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

'Ya'yan 'yar'uwarki zaɓaɓɓiya

A nan, Yahaya na magana game da ikilisiyar da ke tare da shi kamar 'yar'uwar wanda take karanta watsiƙar shi, da kuma masubi da ke tare da ita kamar 'ya'yan ta ne. Wannan na nanata cewa dukan masubi 'ya'yan iyali ɗaya ne cikin ruhu . (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)