ha_tn/2jn/01/07.md

884 B

Mahaɗin Zance:

Yahaya ya gargaɗe su game da masu yaudara, ya tunashe su domin su cigaba cikin koyaswar Almasihu, kuma ya gargaɗesu da su guje wa waɗanda ba su tsaya cikin koyaswa na Almasihu ba.

Gama masu yaudara sun fito a duniya

"Gama malaman ƙarya dayawa sun bar cikin taron" ko "Gama masu yaudara dayawa suna cikin duniya"

masu yaudara

"malamen ƙarya dayawa" ko "masu ruɗi dayawa"

Yesu Almasihu yazo ne a cikin jiki

Zuwa cikin jiki kalmomi ne da aka mora domin nuna ainihin mutum. AT: "Yesu Almasihu ya zo ne a matsayin ainihin ɗan Adam" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Wannan ne mayaudari da kuma magabcin Almasihu

"Su ne waɗanda suka yaudari wasu suka kuma ki goyon bayan Almasihu kansa"

Ku dubi kanku

"Yi la'akari" ko "Maida hankali"

rasa abubuwa

"rasa lada mai zuwa a sama"

dukan sakamako

"cikakken sakamako a sama"