ha_tn/2jn/01/01.md

1.3 KiB

Muhimmin Bayani:

Bisa ga al'ada, Yahaya manzo ne marubucin wannan wasiƙar. Kodashike yana iya yiwuwa ya rubuta zuwa ga wata mace ce, amma domin ya rubuta cewa su "ƙaunaci juna", mai yiwuwa wannan zuwa ga wata ikilisiya ce.

Daga dattijon zuwa ga uwar gida zaɓaɓɓiya da 'ya'yanta

Haka ake fara rubuta wasiƙa. Ana iya bayyana sunan marubucin. AT: "Ni, dattijo Yahaya, ina rubuta wannan wasiƙar zuwa ga uwar gida zaɓaɓɓiya da 'ya'yanta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

dattijon

Wannan na nufin Yahaya ne, manzo da kuma almajirin Yesu. Ya kira kansa "dattijo" domin tsufansa ne ko kuma domin shi shugaba ne na ikilisiya.

zuwa ga uwar gida zaɓaɓɓiya da 'ya'yanta

Mai yiwuwa wannan na nufin taron jama'a da kuma masubi da suke a wurin. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

wanda nake ƙauna cikin gaskiya

"ku, mutanen da nake ƙauna da gaske"

wanda suka san gaskiyar

waɗanda suka san gaskiya game da Allah da kuma Yesu

Uba ... Ɗa

Waɗannan muhimman sunaye ne da ke bayyana dangantaka tsakanin Allah da kuma Yesu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)

cikin gaskiya da kuma ƙauna

Kalmar nan "gaskiya" ta na bayyana "ƙauna." Mai yiwuwa ana nufin "cikin kauna ta gaskiya." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-hendiadys)