ha_tn/2co/09/01.md

888 B

Mahaɗin zance:

Bulus ya cigaba da zancen bayaswa . Yana so ya tabbatar da an yi bayaswa domin masubi dake bukata a Urushalima kafin ya zo saboda da kada ya zama kamar ya ci zarafin su. Ya yi magana game da yanda bayarwa ke albarcance mai bayarwa da kuma daukaki Allah.

Muhimmin bayani:

Yayin da Bulus ke ambata Akaya, ya na nufin lardin Romawa da ke a kudancin Greece inda Korontus yake. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

hidima domin masubi

Wannan na nufin karban kuɗi domin a ba wa masubi a Urushalima. Ma'anan wannan zance na a bayyane. AT: "hidiman bishara ga masubi a Urshalima" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Akaya sun riga sun shirya

Anan kalmar "Akaya" na nufin mutane da suke zama a wannan lardin, masamman mutane na iklisiyar Koronti. AT: "mutanen Akaya su na ta shiri" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)