ha_tn/2co/08/08.md

803 B

ta wurin kwatanta ta da himmar sauran mutane

Bulus na karfafa Korantiyawa cewa su yi yalwar bayarwa ta wurin kwatanta yalwar bayarwar su da na ikklisiyar Makidoniya. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

alherin Ubangijinmu

A wannan halin, kalmar nan "alheri" na nanata yalwar bayarwa wanda Yesu ya albarƙaci Korantiyawa da su.

Kodashike shi mai arziki ne, amma ya zama matalauci domin ku

Bulus ya yi magana game da Yesu kamin zuwansa a jiki ne a matsayin mai arziki, da kuma ɗaukan jikin mutum da yayi a mastayin zaman talaka. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ta wurin talaucinsa ku yi arziki

Bulus ya yi magana cewa Korantiyawa sun zama da arziki ta ruhania ta dalilin bayyanuwar Yesu a jikin mutum. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)