ha_tn/2co/05/01.md

1.8 KiB

Haɗadiyan Bayyani:

Bulus a ciga da nuna bambanci tsakanin jikunan masubi ta wannan duniya da kuma na sama wanda Allah zai bayar.

idan wannan gidan ta duniya da muke zaune a ciki ta rushe, muna da wani gini daga wurin Allah

A nan "gida ta duniya" zuwa wani lokaci ƙayadadde kwatanci ce ta jikin mutum. Anan dauwamammen "gini daga wurin Allah" kwatanci ce ta sabon jiki da Allah zai ba wa masu gaskantawa da shi bayan sun mutu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

in gidan duniya da muke cikin ta ta rushe

Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "in mutane sun rushe gidan mu ta duniya wanda muke ciki" ko "in mutane sun kashe jikunan mu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Gida ce wanda ba da han mutum aka gina ba

Ma'ana "gidan" anan abu daya da "gini daga Allah." "Hannu" anan misali ce dake nufin gabadayan mutum. Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Gida ce wanda ba mutane ne suka yi ba" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]])

cikin wannan bukka muna nishi

"wannan Bukka" na nufin abu daya ne da "gidan da muke ciki a wannan duniya." Kalman nan nishi wata ƙara ce wanda wani kan yi a sa'ada su na sa begen samun wani abu mai kyau.

jira a suturta mu da wurin zaman mu na samaniya

Kalmomin nan "gidan mu na samaniya" na nufin abu daya ne da "gida ne daga Allah." Bulus yayi maganar sabon jiki da masubi za su samu bayan mutuwar su kamar wata gini da kuma sutura da mutum zai iya sa wa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ta wurin sawa

"ta wurin sa gidanmu na samaniya"

ba za a same mu tsirara ba

Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. "baza mu zauna tsirara ba" ko " Allah ba zai same mu tsirara ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)