ha_tn/2co/03/17.md

983 B

Yanzu dukan mu

A nan kalman nan "mu" na nufin dukan masubi har da Bulus da kuma Korantiyawa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

da fuskoki marasa mayafi, muna ganin ɗaukakar Ubangiji

Ba kamar Israila ba wanɗanda ba su iya ganin ɗaukakař Allah kamar yadda ta bayyana a fuskar Musa ba domin ya rufe ta da mayafi, babu wani abu da zai hana masubi ganin ɗaukakar Allah da kuma fahimtar ta. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Muna samun sakewa zuwa cikin irin wannan daukaka

Ruhun na sake masubi su zama da ɗaukaka kamar shi. Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu nuna kuari. AT: "Ubangiji na sake mu cikin ɗaukaka kamar sa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

daga wata mataki na ɗaukaka zuwa ga wata matakin

"daga wata yawan ɗaukaka zuwa ga wata yawan ɗaukaka." Wannan na nufin Ruhun na cingaba da kara ɗaukakan masubi.

kamar dai daga wurin Ubangiji

"kamar dai wannan ta zo daga wurin Ubangiji"