ha_tn/2co/03/14.md

2.2 KiB

Amma zukatan su ta zama a rufe

"Amma sun taurara zukatan su." Bulus ya yi magana game da zukatan Israila kamar wani abu ne da zai iya rufuwa ko kuwa tauri. Wannan na nufin ba su iya fahimtar abin da suka gani ba. AT: "Amma Isa'ila ba su iya fahimtar abin da suka gani ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Gama har wa yau... Amma ko a yau

Waɗannan na maganganu na nufin lokacin da Bulus ke rubutun sa zuwa ga Korantiyawa.

mayafin na nan sa'adda suke karanta tsohon alkawari

kamar yadda Israila basu iya ganin fuskar Musa ba domin ya rufe fuskar sa da mayafi, akwai wani mayafi na ruhu da ke hana mutane fahimtar tsohon alkawarin a sa'ada suka karanta. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

a sa'ada suka karanta tsohon alkawari

"a sa'ada sun ji wani na karanta tsohon alkawari"

ba a cire ta ba domin tawurin Almasihu ne kadai akan fid da ita

A nan bayyanuwan kalman nan "ita" na nufin "mayafin." Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi ma su nuna kuzari. AT: "Babu wanda ke cire mayafin domin tawurin Almasihu ne kadai Allah ke cire ta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

duk lokacin da ake karanta Musa

A nan kalman nan "Musa" na nufin dokokin Tsohon Alkawari. Wannan ana iya bayyana ta cikin Kalmomi masu nuna kuzari. AT: duk sa'ada wani ya karanta dokokin Musa" (See: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

mayafin ta rufe zukatan su

A nan Kalman nan "Zukata" na misalin tunanin mutane, da kuma an yi maganar rashin fahimtar tsohon Alkawarin ga mutanen kamar wata mayafine da ta rufe zukatan su kamar yadda mayafi zai rufe idan su. AT: "ba su iya fahimtar abin da suka ji ba" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

sa'adda mutum ya juyo wurin Ubangiji

A nan "juyo wurin" na da ma'anan biyayya ga wani. AT: " sa'ada mutun ya fara sujada ga Ubangiji" ko "sa'ada mutum ya fara amince da Ubangiji" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

an kawar da mayafin

Allah ya ba su iyawa don su fahimta. Wannan maganan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu nuna kuzari. AT: "Allah ya cire mayafin" ko "Allah ya basu iyawa don su fahimta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)