ha_tn/1ti/03/11.md

1.2 KiB

Hakanan ma mata

Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "mata" na nufin matan dikinoni, ko 2) "mata" na nufin dikinoni da ke mata.

kasance da mutunci

"hali mai kyau" ko "cancanci girmamawa"

Bai kamata su zama magulmanta ba

"Bai kamata suna muguwar magana game da wasu ba"

zama da kamewa

"ba tare da aikata fiye da yadda ya kamata ba." dubi yadda aka fasara wannan cikin 1Timoti 3:2

maza masu mata ɗaya-ɗaya

Dole na miji ya kasance da mata ɗaya. Ba a bayana a fili ba ko wannan ya shafi wanda ya taɓa kasancewa gwauro ko wanda aurensa ya mutu, ko wanda bai taɓa aureba. Dubi yadda aka fasara wannan cikin 1 Timoti 3:2

kulawa da 'ya'yansu da iyalinsu

"tafiyad da yaran da kyau da wasu da ke zama a gidajen su"

ga waɗanda

"ga dikinoni waɗanda" ko "ga waɗannan shugabanen Ikilisiya"

samo wa kansu

"sama wa kansu" ko "ribato wa kansu"

tsayawa mai kyau

Ana iya nuna ainihin ma'anar wannan a fili. AT: "suna mai kyau a cikin sauran masubi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

gabagaɗi cikin bangaskiyar da ke cikin Almasihu Yesu

Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) za su amince da Yesu sosai, ko 2) za su yi magana da gabagaɗi wa wasu mutuna game da bangaskiya a cikin Yesu.