ha_tn/1ti/03/08.md

1.5 KiB

Dikinoni su ma

"Dikinoni, kamar Shugabanen Ikilisiya"

kasance da halin mutunci, ba masu magana biyu ba

Bulus na magana game da waɗanan mutanen kamar suna magana biyu ko suna faɗan abubuwa biyu a lokaci guda. Yana nufin cewa mutumin na faɗin abu amma yana nufin wani abu dabam. AT: " kasance da rayuwa mai kyau da kuma tabbatar da maganarsa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Su zama masu riƙon bayyananniyar gaskiyar

"Dole su cigaba da gaskata gaskiyar saƙon Allah da ke a bayyane gare mu da kuma masubi." wannan na nufin gaskiyar da ke nan a da amma Allah ya nuna masu a wannan lokaci. Bulus na maganar gaskiyar koyarwa game da Allah kamar wani abu ne da mutum ke iya ajiye wa a wurinshi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

bayyananniyar gaskiyar

AT: "gaskiyar da Allah ya bayyanar" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

bangaskiya da lamiri mai tsabta

Bulus na maganar sanin mutum cewa bai aikata wani laifi ba kamar wannan sanin ko lamirin na da tsabta. AT: bangaskiyar sanin cewa sun yi iyakar ƙoƙarinsu su aikata abun da ke daidai" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Daidai ne kuma a tabbatar da su tukuna

AT: "Dole ne sauran masubi su amince da su tukuna" ko "su nuna tabbacin kansu tukuna" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

kasance tabbatace

Wannan na nufin sauran masubi ma su kimanta waɗanda suke so su zama dikinoni, su kuma yanke shawara ko sun yi daidai su yi hidima a cikin Ikilisiya.