ha_tn/1ti/03/01.md

815 B

Mahaɗin Zance:

Bulus ya bayar da muhimman umurnai game da yadda rayuwa da halin masu kulla da ikilisiya ya kamata ya kasance.

aiki mai kyau

"aiki mai daraja"

miji mai mace ɗaya

Dole shugaban Ikilisiya ya kasance mai mata ɗaya. Ba a bayana a fili ba ko wannan ya shafi wanda ya taɓa kasancewa gwauro ko wanda aurensa ya mutu, ko wanda bai taɓa aureba.

Wajibi ne ya zama mai kamewa, mai hankali, mai natsuwa mai karbar baƙi

"kada ya zama mai aikata abubuwa fiye da yadda ake buƙata, mai aikata abu mai ma'ana, mai ɗa'a, ya kuma zamanto abokin baƙi"

Kada ya zama mashayin giya, da mai tankiya, a maimakon haka ya zama da natsuwa, mai salama

"kada ya zama mashayin barasa ko mai son yin faɗa da gardama, maimakon haka ya kasance mai ɗa'a da salama"

mai ƙaunar kuɗi

"haɗamar kuɗi"