1.7 KiB
Ina danƙa wannan umurni a gareka
Bulus na magana game da umurnin kamar wani abu ne da ya sa a gaban Timoti wanda ana iya gani. AT: "ina danƙa maka wannan umurnin" ko "wannan umurni ne nake ba ka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)
ɗa na
Bulus na bayyana dangantakarsa da Timoti kamar na Uba da ɗansa. Ya yiwu ta hanun Bulus ne Timoti ya karɓi bishara shiya sa Bulus na ɗaukarsa a matsayin ɗa. AT: "wanda yake kamar ɗa na gaske" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)
bisa ga anabcin da aka yi a baya game da kai
AT: "bisa ga anabci game da kai daga sauran masubi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)
yi yaƙi mai kyau
Bulus na magana game da aikin da Timoti ke yi wa Ubangiji kamar yaƙi ne da soja ke yi. AT: "cigaba da matukar aiki wa Ubangiji" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)
ƙyaƙƙyawan lamiri
"lamiri da ke zaɓan abu mai ƙyau ba mumuna ba." dubi yadda aka fasara a 1:5.
wanɗansu suka yi ɓarin bangaskiyarsu
Bulus na magana game da bangaskiyar waɗanan mutane kamar wani jirgi ne da ya yi haɗari a tẽku.Yana nufi cewa sun illatar da bangaskiyarsu, wato basu gaskata cikin Yesu kuma ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)
Himinayas ... Askandari
Wannan sunayen maza ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)
waɗanda na bada su ga shaiɗan
Bulus na magana kamar ya danka mutanen wa Shaiɗan fuska da fuska. Ya yiwu Bulus ya ƙi amincewa da su a cikin al'umman masubi. Dashike sun bar iyalin masubi Shaiɗan na da iko akan su, kuma zai iya yi masu illa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)
su iya koyi
AT: "Allah ya koyar da su" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)