ha_tn/1ti/01/05.md

1.6 KiB

Yanzu

An yi amfani da wannan kalman domin a dakatar da ainihin koyarwa da a ke yi. Anan Bulus ya bayyana manufar umurni da yake ba wa Timoti.

umurnin

Anan wannan baya nufin Tsohon Alkawari ko dokoki goma amma umurni ne da Bulus ya bayar a 1Timoti 1:3-4.

ƙauna ce

AT: "ƙauna ce zuwa Allah" ko "a ƙaunaci mutane."

daga sahihiyar zuciya

A nan "sahihiya" na nufi cewa mutum ba shi da wata muguwar manufa a ɓoye. "zuciya" kuma anan na nufin tunani da hankalin mutum. AT: "daga tunani mai kyau" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

lamiri mai kyau

"lamiri da ya zaɓi abu mai kyau ba mumuna ba"

sahihiyar bangaskiya

"bangaskiya na gaske" ko "bangaskiya ba tare da munafurci ba"

Waɗansu sun kauce daga hanya

Bulus na magana game da bangaskiya cikin Almasihu kamar wata buri ne da a ke nufa. Bulus na nufin cewa waɗansu mutane basu cika manufar bangaskiyar su ba, wanda shine ƙauna, kamar yadda ya faɗa a 1:5. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

sun juya zuwa ga waɗanan abubuwa

A nan "juya zuwa" na nufin cewa sun daina yin abun da Allah ya umurta. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Malaman shari'a

A nan "shariya" na nufin shari'ar Musa.

amma basu fahimta ba

"ko da yake basu fahimta ba" ko "basu fahimta ba tukuna"

abin da suka tsaya akai

"abin da suka amince a kan gaskiya"

Amma mun sani cewa shariya tana da kyau

"mun fahimci cewa shariya tana da amfani"

idan an yi amfani da ita bisa ka'ida

"idan mutum yayi amfani da ita yadda ya kamata" ko "idan mutum yayi amfani da ita yadda Allah ke so"