ha_tn/1ti/01/01.md

1.5 KiB

Muhimmin Bayani

A wannan littafi sai dai in an faɗa amma, kalma "mu" na nufin Bulus ne da Timoti (wanda aka rubutawa wannan wasiƙan), da kuma dukan masubi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

Bulus manzo

"Ni, Bulus manzo marubucin wannan wasiƙa." Ya yiwu akwai yadda ake gabatar da marubucin wasiƙa a harshe ku, toh ayi amfani dashi a nan. In ya zama lalle za a iya faɗa wanene ake rubutawa wasiƙan.

bisa ga umurnin

"daga dokan" ko "ta wurin ƙarfin ikon"

Allah mai ceto

"Allah wanda ya cece mu"

Almasihu Yesu begenmu

A nan "begenmu" na nufin mutumin da muke da bege a kansa. AT: "Almasihu Yesu wanda a cikin shi ne muke da bege" ko "Almasihu Yesu wanda mun gaskata" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

yaro na gaske cikin bangaskiya

Bulus na magana game da dangantakarsa da Timoti kamar na wani Uba da ɗansa. Wannan ya nuna sahihiyar ƙauna da amincewa da Bulus ke dashi game da Timoti. Ya yiwu kuma ta hannun Bulus ne Timoti ya karɓi ceto shiya sa Bulus ya ɗauke shi a matsayin ɗansa. AT: "wanda yake kamar ɗa a wurina" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Alheri, jinkai, da salama

"Bari alheri, jinkai, da salama su kasance da kai," ko "Bari ka kasance da kyan zuciya, jinkai, da salama"

Allah Uba

"Allah, wanda shine Ubanmu." A nan "Uba" muhimmin suna ne na Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)

Almasihu Yesu Ubangijimu

"Almasihu Yesu, wanda shine Ubangijimu"