ha_tn/1th/04/09.md

1.2 KiB

ƙaunar 'yan'uwa

"ƙaunar 'yan'uwa masubi"

kunayin wannan ga dukkan 'yan'uwa waɗanda suke cikin dukkan Makidoniya

"kuna nuna ƙauna zuwa ga dukkan masubi da suke Makidoniya"

biɗa

"yi ƙoƙari"

zauna a natse

Bulus yayi amfani da kalman "natse" da nufin zaman salama cikin al'umma ba tare da jayayya ba. AT: "zama cikin natsuwa da kuma yadda ya kamata"

kula da al'amuranku

"ku yi aikinku" ko " ku kula da abubuwan da ke alhakinku ku yi. Wannan na iya nufin da cewa kada mu dinga tsegumi da kuma tsoma baki a al'amuran wasu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

kuyi aiki da hannuwanku

Wannan na nufin yin rayuwa mai ribatowa. AT: "yi na ku aikin domin samun abin da kuke bukata na zaman rayuwa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

tafiyar da ta dace

A nan "tafiya" na nufin "rayuwa" ne ko kuma "nuna hali." AT: "nuna halin da ya dace" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

dace wa

ta hanyar nuna girmamawa ga wasu da kuma samun girmamawansu.

a gaban 'yan waje

Bulus na magana game da waɗanda basu bada gaskiya a cikin Almasihu ba kamar suna wajen wani wuri ne da masubi ke ciki. AT: "a idanun waɗanda basu ba da gaskiya cikin Almasihu ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)