ha_tn/1th/03/11.md

1.2 KiB

Muhimmin Bayani:

A wannan ayoyin, kalman "mu" baya nufin ƙungiyar mutane ɗaya a kowane lokaci. A yi lura da fassara domin a gane ainihin ma'ana.

Bari Allahnmu ... Ubangijinmu Yesu

Bulus ya haɗa masubi na Tassalonika da abokan aikinsa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

Bari Allahnmu

"Muna addu'a cewa Allahnmu"

bi da hanyanmu zuwa gare ku

Bulus na magana kamar yana so Allah ya nuna masa da tawagarsa hanyar da zasu bi domin ziyarar masubi da ke Tasalonika. Yana nufin cewa, yana so Allah ya ba su zarafin yin haka. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Uba da kansa

A nan "kansa" na nufin Uban ne, an yi haka domin nanaci ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rpronouns)

ƙaru ku kuma ribambanya a ƙauna

Bulus na magana game da ƙauna kamar wani abu ne da ake samuwa sannan a iya ƙarawa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ƙarfafa zukãtanku, domin su kassance

A nan "zuciya" na nufin abin da mutum ya yarda dashi, ya kuma amince da shi. AT: "ƙarfafa ku, domin ku zama" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

a lokacin zuwan Ubangijinmu Yesu

"a lokacin da Yesu ya dawo duniya"

tare da dukkan tsarkakansa

"tare da dukkan waɗanda suke nasa"