ha_tn/1sa/19/12.md

548 B

Muhimmin Bayani:

Mikal ta taimaka wa Dauda ya tsere wa Sarki Saul. Tana amfani da gunkin gida don yin gadon Dauda kamar yana kwana a ciki.

Sai ta sanya matashin kai na gashin akuya akansa, ta kuma rufe shi dakayayyaki

Zai yiwu ma'anonin su 1) kan gunkin yana kwance kan matashin gashin akuya kuma Mikal ta sanya gunkin a cikin kayan Dauda ko 2) Mikal ta yi amfani da tufafin Dauda a matsayin bargo don ta rufe gunkin gaba ɗaya kuma ta yi "matashin kai" na akuyar gashi yayi kamar gashin Dauda wanda ya fito daga ƙarƙashin bargon tufafi.