ha_tn/1pe/04/17.md

2.0 KiB

iyalin Allah

Wannan na nufin masubi wadda Bitrus ya yi magana game da su cewa su iyalin Allah ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Idan kuwa za a fara da mu, menene ƙarshen waɗanda suka yi rashin biyayya da bisharar Allah?

Bitrus ya yi amfani da wannan tambaya don ya nanata cewa shari'a Allah zai fi tsanani ga mutane da suka ƙi bishara na masubi. AT: "Idan kuwa an fara da mu, lailai abin da zai zama ga waɗanda sun yi rashin biyayya ga bisharar Allah zai zama da muni." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

to me zai zama ga waɗanda

"me zai faru da waɗanda"

waɗanda sun yi rashin biyayya ga bisharar Allah

"waɗanda ba su gaskata da bisharar Allah ba." A nan kalman nan "biyayya" na nufin gaskatawa.

"mai adalci ... me zai faru da marar bin Allah da mai zunubi kuma?

Bitrus ya yi amfani da wannan tambaya don ya nanata cewa masu zunubi za su sha wahala fiye da masubi. AT: "mutum mai adalci ... abin da zai haifar wa mara bin Allah da masu zunubi zai fi muni." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

me zai zama ga marasa bina Allah da masu zunubi

me zai faru da marasa bin Allah da masu zunubi"

in har mai adalci ya tsira da kyar

A nan kalman nan "tsira" na nufin ceto na ƙarshe a sa'ad da Alamasihu ya dawo. AT: "In har mutum mai adalci ya sha wuya kafin Allah ya cece shi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

marar bin Allah da mai zunubi kuma

Kalmomin nan "mara bin Allah" da "mai zunubi na nufin abu ɗaya, su na kuma nanata muguntar waɗannan mutanen. AT: marasa bin Allah, masu zunubi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)

su miƙa rayukansu

A nan kalman nan "rayuka" na nufin mutum gabadayansa. AT: "miƙa kansu" ko "miƙa ransu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

yin ayuka nagari

Ana iya juya "yin ayuka nagari" cikin fi'ilin magana. AT: "sa'and da suke nagargarun ayuka" ko "sa'and da suke rayuwa da ta cancanta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)