ha_tn/1pe/04/07.md

1.4 KiB

Ƙarshen dukan abubuwa

Wannan na nufin ƙarshen duniya loƙacin zuwan Almasihu ta biyu.

na zuwa

An yi magana game da ƙarshen da zai zo ba jimawa sai kace ya na zuwa kurkusa daga nesa. AT: "zai faru ba da jimawa ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ku zama natsatsu, ku natsu cikin tunaninku

Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne. Bitrus ya yi amfani da su don ya nanata bukatar yin tunani game da rayuwa da shike ƙarsehn duniya ta kusa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)

ku natsu cikin tunaninku

A nan kalman nan "natsu" na nufin ba shakka cikin hankali da kuma zaman shiri. Dubi yadda ku ka jiya wannan cikin [1 Bitrus 1:13]. AT: "ku sarrafa tunanin ku" ko " ku yi hankali da abin da kuke tunaninsu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Fiye da kome

"Mafi muhimmanci duka"

domin ƙauna tana rufe laifofin masu ɗumbin yawa

Bitrus ya bayyana "ƙauna" sai ka ce wai mutum ne wanda ke sa murfi kan laifofin wasu. Ma'anoni masu yiwuwa 1) "gama mutumin da ke ƙauna kuwa ba zai taɓa yi ƙoƙarin neman sanin ko wani ya yi zunubi ba" ko 2) "gama mutumin da ke ƙauna zai yafe laifofin sauran mutane, ko su na da yawa" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-personification]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

Ku yi wa juna bakunta

Ku yi wa juna kirki ku kuma marabci baƙi da matafiye