ha_tn/1pe/03/21.md

1020 B

Wannan kwatancin baftismar da take cetonmu yanzu

Bitrus ya ce baftisma ta yi daidai da hanyar da Allah ya ceci Nuhu da iyalinsa cikin jirgin daga ruwan tsufana.

baftismar da ta cece ku yanzu

Baftisma hanya ce da Allah ke ceton mutane. AT: "ta wurin baftismar da Allah ya cece ku yanzu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

ta roƙon Allah da lamiri mai kyau

Ma'anoni masu yiwuwa 1) "roƙon mutum ga Allah ya bashi lamiri mai kyau" ko 2) "alkawarin mutum ga Allah wadda aka yi da lamiri mai kyau, wato, da gaske."

ta wurin tashin Yesu Almasihu daga mattattu

"saboda tashin Yesu Almasihu daga mattattu." Wannan maganar ta kammala bayanin cewa "Wannan alama ce ta baftismar da ta cece ku yanzu."

Almasihu yana hanun daman Allah

Zama a "hanun daman Allah" alama ce da ke nufin cewa Allah ya ba wa Yesu babbar daraja da iko bisa kowa. AT: "Almasihu na gefen Allah cikin wurin ɗaukaka da iko" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

yi masa biyayya

"yi wa Yesu biyayya"