ha_tn/1pe/03/10.md

2.0 KiB

yake so ya more rayuwarsa ya kuma ga kwanaki masu alheri

Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne kuma na nanata sha'awar samun rayuwa mai kyau. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)

ga kwanaki masu alheri

A nan an yi maganar samun abubuwa masu kyau kamar ganin abubuwa masu kyau. Kalmar nan "kwanaki" na nufin dukan rayuwar mutum. AT: "samun abubuwa masu kyau cikin rayuwa" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]])

ya kame harshen sa daga mugunta da leɓensa daga maganganun yaudara

Kalmomin nan "harshe" da "leɓe" na nufin mutumin da ke magana. Waɗannan na nufin abu ɗaya na kuma nanata dokan cewa kada ka yi karya. AT: "daina faɗin mugayen abubuwa da kuma abubuwa yaudara" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]])

Ya juyo daga mugunta

A nan "juyo" na nufin a bar yin wani abu. AT: "ya bar aikata abu mara kyau" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Idanun Ubangiji suna duban adalai

Kalman nan "idanu" na nufin iyawar Ubangiji na sanin abubuwa. An yi maganar cewa Ubangiji ya yarda da adalai kamar yana ganin su. AT: "Ubangiji na ganin adalan" ko "Ubangiji ya yarda da adalai" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

kunnuwansa kuma suna sauraron roƙe-roƙensu

Kalman nan "kunnuwa" na nufin cewa Ubangiji ya na sane da abin da mutane ke faɗi. Cewar Allah na jin maganar roƙe-roƙensu na nufin cewa yana kuwa amsa su. AT: "yana jin roƙe-roƙensu" ko "yana amsa roƙe-roƙensu" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]])

fuskar Ubangiji tana gaba da

Kalmar nan "fuska" na nufin nufin Ubangiji ya yi gaba da maƙiyansa. An yi maganar gaba da wani kamar a ce an sa fuskar wani gaba da mutumin. AT: "Ubangiji na gaba" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])