ha_tn/1pe/03/08.md

1019 B

haɗa hankulanku

"ku zama masu ra'ayi ɗaya ku kuma" ko "zama masu hali iri ɗaya ku kuma"

taushin zuciya

zama masu hankali da tausayi ga waɗansu

Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi

Bitrus ya yi magana a kan daukan mataki game da halin wani mutum kamar biyan bashin waɗannan halayyan. AT: "Kada ku yi mugunta ga wani wanda ya yi muku mugunta ko kuwa zagi ga wanda ya zage ku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

cigaba da sa albarka

Kuna iya bayyanawa a fili wanda da za a sa masa albarka. AT: "ku cigaba da sa wa waɗanda suka yi muku mugunta ko sun zage ku, albarka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

sabili da haka ne musamman aka kiraye ku

AT: "sabili da wannan ne Allah ya kiraye ku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

domin ku gaji albarka

Bitrus ya yi maganar samun albarkan Allah kamar karɓar gado ce. AT: "don ku karɓi albarkar Allah a matsayin dauwamammen mallaka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)