ha_tn/1pe/03/01.md

1.5 KiB

Muhimmin Bayani:

Bitrus ya fara magana da matan aure.

Haka kuma ku da kuke matan aure, kuyi biyayya ga na ku mazajen

Daidai kamar yadda masubi za su yi "biyayya ga kowane hukuma ta mutane" [1 Bitrus 2:13] da kuma bayi su "yi biyayya" ga iyayen gijinsu [1 Bitrus 2:18], matan aure su yi biyayya ga mazajen su. Kalmomin nan "biyayyay", "bin" da kuma "mika kai" ana iya juya su ta wurin yin amfani da kalma ɗaya.

waɗansu mazajen basu biyayya da maganar

A nan "maganar" na nufin saƙon bishara. Rashin biyayya na nufin basu gaskata ba. Dubi yadda ku ka juya magana makamancin haka cikin [ 1 Bitrus 2:8]. AT: "Waɗansu mazaje basu gaskata da saƙo game da Yesu ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

shawo kansu

"mai yiwuwa a rinjaye su su gaskata da Almasihu." Wannan na nufin cewa mazajensu da ba su gaskata ba za su zama masubi. AT: "za su iya zama masubi" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-idiom]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

ba tare da magana ba

"ba tare da matan ta yi wani magana ba." A nan "magana" na nufin wani abin da matan za ta iya faɗa game da Yesu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-ellipsis)

Domin sun ga tsattsarkan halinku da ladabinku

Wannan kalmar "halinku" ana iya juya ta cikin aikatau. AT: "za su gani cewa kuna da tsattsarkan hali da ladabi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

tsattsarkan halinku da ladabi

Ma'anoni masu yiwuwa 1) "tsattsarkan halinku gare su da kuma yadda kuke girmama su" ko 2) "tsantsan halinku gare su da kuma yadda kuke girmama Allah."