ha_tn/1pe/02/01.md

1.8 KiB

Mahaɗin Zance:

Bitrus ya cigaba da koyar da masu karanta wasiƙar sa game da tsarki da kuma biyayya.

Saboda haka sai ku tuɓe dukkan keta, rikici, da riya, kishi, da dukkan mugun zance

An yi maganar waɗannan ayukan zunubi kamar waɗansu abubuwa ne da mutane ke iya wurgawa. Kalman nan "Soboda haka" na nufin komawa zuwa ga abinda Bitrus ya faɗa game da zaman tsarki da biyayya a baya. AT: "don haka, ku tuɓe kowane mugun abu, da riya, da ƙishi, da kowane mugun zance" ko "don haka, ku bar aikata mugunta, ko ruɗu, ko riya, ko ƙishi ko mugayen zance" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Kamar jarirai, sababbin haihuwa, ku yi marmarin madara na ruhaniya

Bitrus ya yi magana da masu karanta wasiƙar sa kamar jarirai. Jarirai suna bukatar tsantsan abinci wanda za su iya narkewa da sauki. haka kuma masubi suna bukatar tsantsan koyarwar daga maganar Allah. AT: Kamar yadda jarirai suna marmarin mama daga uwarsu, haka kuma lallai ne ku yi marmarin tsantsan madaran ruhaniya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

marmarin

"matuƙar marmari" ko "yi begen"

tsantsan madaran ruhaniya

Bitrus ya yi magana game da maganar Allah kamar wata madaran ruhaniya ce da ke da amfani sosai ga 'ya'ya (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

domin kuyi girma zuwa ceto

A nan kalmar nan "ceto" na nufin a sa'ad da Allah ya kammala ceton mutanensa a lokacin da Yesu ya dawo (Dubi 1 Bitrus 1:5).

girma

Bitrus ya yi maganar karuwa cikin sanin Allah da kuma amincin masubi ga Allah kamar su 'ya'ya ne da ke girma. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

idan kun ɗanɗana Ubangiji mai alheri ne

A nan ɗanɗana na nufin mutum ya jin abu da kansa. AT: "In ka ji alherin Ubangiji zuwa gare ka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)