ha_tn/1ki/22/03.md

849 B

''Ko kun san Ramot Gileyad tamu ce, amma ba ma yin komai domin mu ƙwace ta daga hannun sarkin Aram?'

Ahab ya yi wannan tambayar ya jaddada cewa ya kamata da sun riga sun ƙwace Ramot da Gileyad. AT: "Ramot Gileyad tamu ce, amma ba ma yin komai domin mu ƙwace ta daga hannun sarkin Aram?" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

ƙwace ta daga hannun sarkin Aram

A nan kalmar "hannu" na nufin iko. AT: "mu ɗauke shi daga jagorancin sarki Aram" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ni kamar ka ne, mutanena kuma kamar mutanenka ne, dawakaina suna kamar naka ne

Yehoshafat ya gaya wa Ahab cewa da shi, da mutanensa da dawakansa na Ahab ne, ma'ana Ahab zai iya shugabantarsu yadda ya so. AT: "Ni, sojojina, da dawakaina naka ne ka yi amfani da su ta kowacce hanya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)