ha_tn/1jn/05/09.md

1.2 KiB

Idan mun karbi shaidar mutane, shaidar Allah ta fi girma

Mai fasara na iya ƙarin bayani game da dalilin ya sa yakamata mu gastata da abinda Allah ke faɗi: AT: "idan mun gaskata da abinda mutane ke faɗi, toh sai mu gaskata da abinda Allah ke faɗi domin shi mai faɗin gaskiya ne a ko da yaushe" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

karɓi shaidar mutane

Wannan, wato "karɓi shaidar", na nufin a gaskata da abinda wani ke faɗi game da wani abinda ya gani. AT: "gaskata da abinda mutane sun shaida" ko kuma "gaskata abinda mutane ke faɗi game da abinda suka gani" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-idiom]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-abstractnouns]])

shaidar Allah ta fi girma

shaidar Allah ta fi muhimmanci da abin dogaro

Ɗan

Wannan wata suna ce ta Yesu, Ɗan Allah (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)

Wanda ya gaskata da Ɗan Allah shaidar tana nan tare da shi

"Duk mai gaskata da Yesu ya sani da tabbaci cewa Yesu Ɗan Allah ne"

ya mai da shi maƙaryaci kenan

"ya ce da Allah maƙaryaci"

domin bai gaskata da shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba

"domin bai gaskata cewa Allah ya faɗi gaskiya game da Ɗansa ba"