ha_tn/1jn/05/06.md

824 B

Mahaɗin zance:

Yahaya yana koyarwa a kan Yesu Almasihu da kuma abinda Allah ya faɗi game da shi.

Wannan shine wanda yazo ta wurin ruwa da jini: Yesu Almasihu

Yesu Almasihu shi ne wanda ya zo ta wurin ruwa da jini. A nan "ruwa" na iya nufin baftismar Yesu, "jini" kuma na iya zama alama ce ta mutuwar Yesu a bisa giciye. AT: "Allah ya nuna cewa Yesu Almasihu Ɗansa ne ta wurin baftismar Yesu da mutuwarsa a bisa giciye" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ya zo ba ta wurin ruwa kadai ba, amma ta wurin ruwa da jini

A nan "ruwa" na nufin baftismar Yesu, "jini" kuma na iya zama alama ce ta mutuwar Yesu a bisa giciye. AT: "Ba ta baftisma ne kawai Allah ya nuna mana cewa Yesu Ɗansa ba ne, amma ta wurin baftismarsa da mutuwarsa a bisa giciye" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)