ha_tn/1jn/05/04.md

1.2 KiB

Duk wanda yake haifaffe na Allah yakan yi nasara

"duk 'ya'yan Allah sukan yi nasara"

nasara da duniya

"na da nasara a kan duniya" ko kuma "suna kin aikata miyagun abubuwan da marasabi ke yi"

duniya

A nan "duniya" na nufin dukan mutane masu aikata zunubi da kuma sha'anin miyagu da ke duniya. AT: "dukan abin duniya da ke gãba da Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Wannan itace nasarar da ta rinjayi duniya, wato bangaskiyarmu

"Wannan itace abinda ke bamu ikon tsayayya da duk abinda zai kai mu ga yi wa Allah zunubi: bangaskiyar mu" ko kuma "Bangaskiyar mu ne ke bamu ikon tsayayya da duk abinda zai kai mu ga yi wa Allah zunubu"

Wanene wannan mai nasara da duniya?

Yahaya ya yi amfani ne da wannan tambayan ya gabatar da wata sabuwan abu da yake so ya koyar. AT: "Ni zan gaya maku wanda ke mai nasara da duniya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Sai dai wanda ya gaskata Yesu Ɗan Allah ne

Wannan na nufin ko ma wa, duk dai wanda ya gaskata da haka. AT: "Duk wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne"

Ɗan Allah

Wannan wata suna ce mai muhimmanci na Yesu wadda ke bayyana dangantakarsa da Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)