ha_tn/1jn/05/01.md

681 B

Muhimmin Bayani:

Yahaya yana cigaba da koyaswa masu karatun wasiƙarsa game da ƙaunar Allah da kuma ƙaunar da yakamata masubi su kasance da ita domin sun samu wata sabuwan halitta daga Allah.

haifaffe na Allah ne

"ɗan Allah ne"

Haka muka sani muna ƙaunar 'ya'yan Allah: yayin da muka ƙaunaci Allah, kuma muka aikata umarninsa

"Yayin da mun ƙaunaci Allah mun kuma kiyaye umarninsa, toh mun san cewa muna ƙaunar 'ya'yansa"

Wannan itace ƙaunar Allah, cewa mu kiyaye umarninsa

"Domin yayin da mun kiyaye umarninsa, shi ne ƙaunar Allah ta gaskiya"

umarninsa ba masu nawaitawa bane

"Umarninsa ba masu wuya bane"

nawaita

"nauyi" ko "murkushewa" ko "wuya"