ha_tn/1jn/04/17.md

1.5 KiB

Dalilin wannan ƙauna ya zama cikakke a cikinmu, domin mu kasance da gabagaɗi

Wannan na iya nufin 1) "Dalilin wannan" na maida tunanin mu baya zuwa [4:16]. AT: Domin duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna yana cikin Allah, Allah kuma yana cikinsa. Allah ya cika ƙaunar da yake da shi domin mu saboda haka muna da cikakken gabagaɗi" ko kuma 2)"Saboda haka" na nufin "za mu iya samun gabagaɗi". AT: Muna da gabagaɗi cewa Allah zain karɓe mu a ranar da zai shari'anta kowa, don haka mun san irin ƙaunar da yake da shi domin mu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

wannan ƙaunar ta kammala a cikinmu

AT: Allah ya sa ƙaunarsa domin mu yă zama cikakke" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

domin kamar yanda ya ke haka muma muke a cikin duniyan nan

"domin dangantakar da Yesu ke da shi da Allah ɗaya ne da dangantakar da muke da shi da Allah a duniyan nan"

Amma cikkakiyar ƙauna takan kawar da tsoro

A nan an fasara "ƙauna" kamar wani mutum ne da ke da ikon cire tsoro. Ƙaunar Allah kamalalle ne. AT: "Amma sa'and da ƙaunar mu ta cika, ba za mu ji tsoro kuma ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

domin kuwa tsoro na tafiya tare da hukunci

"domin za mu ji tsoro ne kaɗai idan mun san cewa zai hukunta mu"

Amma wanda yake da tsoro ba shi da cikakkiyar ƙauna

AT: "Amma idan mutum yana da tsoron cewa Allah zai hukunta shi, ƙaunarsa bai cika ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)