ha_tn/1jn/03/13.md

1.7 KiB

'yan'uwana

"'yan'uwana masubi." Masu karatun wasiƙar Yahaya maza da mata ne.

idan duniya ta ƙi ku

A nan kalmar nan "duniya" na nufin mutanen da ba su girmama Allah. AT: "idan waɗanda ba su girmama Allah sun ƙi ku masu girmama Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai

An yi maganar sharaɗin rayuwa da na mutuwa kamar wasu wurare ne da mutum zai iya bari ko zuwa. AT: "Mu ba matattu bane a ruhaniya har yanzu amma muna da rai a ruhu" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-abstractnouns]])

rai

Kalmar nan "rai" a wannan wasiƙar gaba ɗaya ya wuci rai na jiki kawai. A nan ya tsaya ne madadin Yesu, rai na har abada. Duba yadda kun fasara wannan a [1:1-2](Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

matacce ne har yanzu

"yana mace a ruhaniya har yanza"

Dukan wanda yake ƙin ɗan'uwansa, mai kisan kai ne

Yahaya yana maganar mutumin da ke ƙin ɗan'uwansa maibi a matsayin mai kisankai ne. Tunda mutanen da ke kisan kai su na yin haka ne don sun ƙi sauran mutanen, Allah yana ɗaukan duk wanda ke ƙin wani a matsayin mai laifi kamar wanda ya kashe mutum ne. AT: Dukan wanda ya na ƙin ɗan'uwansa mai laifi ne daidai da wanda ya ƙashe mutum" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

babu rai na har abada a cikin mai kisankai

"Rai na har abada" wani abu ne da Allah ke ba masubi bayan sun mutu, amma shi ma wani iko ne da Allah ke ba wa masubi a wannan rai don ya taimake su su daina yin zunubi kuma su fara aikata abinda kan gamshe shi. An yi maganar rai na har abada kamar wani mutum ne da na iya zama a cikin mutum. AT: "mai kisan kai ba shi da ikon rayuwa na ruhaniya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)