ha_tn/1jn/02/15.md

1.4 KiB

Kada kuyi ƙaunar duniya ko

A 2:15-17 Kalmar nan "duniya" na nufin dukan abubuwan da mutane ke so su yi da ba su girmama Allah. AT: Kada halin ku ya zama kamar na mutanen da suke cikin duniya da basu girmama Allah, kuma basu ƙauna" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

abubuwan da suke cikin duniya

"abubuwan da waɗanda basu girmama Allah suke so"

Idan wani yayi ƙaunar duniya, ƙaunar Uban bata cikinsa

Mutum ba zai iya ƙaunar duniya da kuma dukan abubuwan da basu darajanta Allah ya kuma ƙaunaci Uban a lokaci ɗaya ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ƙaunar Uban bata cikinsa

"baya ƙaunar Uban"

kwaɗayi na jiki, abin da idanu suke sha'awa, da rayuwar girman kai

Waɗannan sune jerin wasu abubuwan da ke cikin duniya. Sun bayyana abin da ake nufi da "kome da ke cikin duniya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Kwaɗayi na jiki

"samun ƙaƙƙarfan marmarin aikata zunubi"

kwaɗayi na abinda idanu suke sha'awa

"Ƙaƙƙarfan marmarin samun abubuwan da muke iya gani"

rayuwar girman kai

Wannan na iya nufin a mallaka da kuma halayya. AT: "yin alfahari da abinda mutum ke yi ko ke da shi" ko kuma "girman kai da mutane ke yi domin abubuwan da suke da shi da abubuwan da suke yi"

ba daga Uban bane

"basu zo daga Uban ba ne" ko kuma "ba yadda Uban ya koya mana mu yi rayuwa bane"

tana wucewa

"wucewa" ko kuma "watarana ba za a same ta a nan ba"