ha_tn/1jn/02/07.md

1.0 KiB

Ƙaunatattu, Ina

"ku mutane wadda na ke ƙauna, Ina" ko kuma "Ƙaunattun abokai, Ina"

ba sabuwar doka nike rubuta maku ba, amma tsohuwar doka ce

"Na rubuta muku cewa ku ƙaunaci juna, wannan ba wata sabuwar abin yi bane amma tsohuwar dokar da kun taba ji." Yahaya na nufin umurnin Yesu mai cewa a ƙaunaci juna.

tun farƙo

A nan "forƙo" na nufin lokacin da sun yanke shawara su bi Yesu. AT: daga forkon lokacin da kun gaskata da Almasihu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Tsohuwar dokar kuwa itace maganar da kuka ji

"Tsohuwar dokar itace sakon da kuka ji"

Amma yanzu ina rubuta maku sabuwar doka

"Amma a wata hanya dokar da na rubuta maku sabuwar doka ce"

wadda gaskiya ce a cikin Almasihu da cikinku

"wadda gaskiya ce, kamar yadda ta bayyana a cikin halayen Almasihu da halayen ku"

duhu yana wucewa, haske na gaskiya yana haskakawa

A nan "duhu" na nufin "mugunta" kuma "haske" na nufin abu "mai kyau." AT: "domin kuna barin yin mugunta kuna kara yin abu mai kyau" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)