ha_tn/1co/16/13.md

1.3 KiB

Ku zauna a fadake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, kuna nuna halin maza, ku yi karfin hali

Bulus ya na kwatanta abin da yake son Korontiyawan su yi kamar ya na ba wa soja umurni hudu a yaki. Wannan umurni hudun na nufin abu ɗaya kuma ana amfani da su domin nananci. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)

Ku zauna a fadake

Bulus ya yi magana game da mutanin da sun san abin da ke faru kamar sun zama masu tsaro da ke tsaron gari ko kuma lambu. AT: "Yi hankali da wadda kun amince da shi" ko kuma "ku yi hankali da haɗari" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ku tsaya daram cikin bangaskiya

Bulus ya yi magana game da yadda mutane sun cigaba da bin Almasihu bisa koyarwansa kamar sun zama sojojin da sun ƙi su ja da baya a harin makiya. AT: 1) "ku gaskanta da karfi a abin da mun koya maku" ko kuma 2) "ku amince da Almasihu da karfi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

kuna nuna halin maza

A garin da Bulus da masu sauraransa suke, mazaje su na tanada wa iyalin su ta wurin yin aiki mai karfi da faɗa da masu shigan gari da hari. AT: "ku zama da takalifi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Bari dukan abinda kuke yi ayi shi cikin kauna

"Dukkan abin da ku ke yi ya nuna wa mutane cewa ku na kaunan su"