ha_tn/1co/06/12.md

1.1 KiB

Dukkan abu halal ne a gare ni

AT: 1) Bulus ya na amsa abin da waɗansu Korontiyawan za su iya yin tunani, "waɗansu sun ce, 'zan iya in yi komai" ko kuma 2) Bulus ya na faɗan abin da ya ke tunani cewa daidai ne, "Allah ya yarda ma ni in yi komai."

amma ba kowanne abu ne mai amfani ba

Bulus ya na amsa wadda a ce, "kowanne abu halal ne a gare ni." AT: "amma ba kowanne abu ne ya ke da kyau a gare ni ba"

amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba

AT: "ba zan yarda wadanan abubuwa su yi mulki a kai na kamar maigida ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

"Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne", amma Allah zai kawar da su duka

AT: 1) "Bulus ya na gyara abin da waɗansu Korontiyawan za su iya yin tunani, "abinci don ciki, kuma ciki don abinci ne," ta wurin amsa cewa Allah zai kawar da cikin da kuma abincin duka ko kuma 2) Bulus ya yarda cewa "abinci don ciki, kuma ciki don abinci ne," amma ya kara cewa Allah zai kawar da su duka.

Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne

Wannan na iya nufin cewa mai maganan na magana game da jiki da kuma jima'i, amma ku fasara wannan kamar "ciki" da "abinci."

kawar da

"hallaƙa"