[ { "title": "Muhimmin Bayani:", "body": "Elisha ya cigaba da magana da sarki Yowash" }, { "title": "Buɗe tagar da ke wajen gabas", "body": "\"bude wannan taga da ke fuskantar gabas\" ko \"bude wannan taga zuwa gabas\" " }, { "title": "sai ya buɗe ta", "body": "Tunda yake wannan ya faru bayan Yowash ya ɗauki baka da kibau, wataƙila bawa ya buɗe taga. AT: \"Don haka wani bawa ya buɗe shi\" (Duba: figs_explicit)" }, { "title": "Wannan kibiyar nasarar Yahweh ce, kibiyar nasara akan Aram", "body": "Za'a iya bayyana alakar dake tsakanin kibiya da nasara a bayyane. AT: \"Wannan kibiya wata alama ce daga Yahweh cewa ita ce za ta ba ka\nnasara a kan Aram\" ko \"Wannan kibiya tana misalin nasarar da Yahweh zai ba\nka a kan Aram\" (Duba: figs_explicit)" }, { "title": "Afek", "body": "Wannan wani birni ne a kasar Isra'ila. (Duba: translate_names)" }, { "title": "Amma mutumin Allah ya yi fushi da", "body": "\"Amma Elisha yayi fushi da sarki Yowash\"" }, { "title": "har sai ka hallakar da ita", "body": "\"har sai kun halakar da ita gaba ɗaya\" ko \"har sai an shafe su gaba ɗaya\"" } ]