[ { "title": "Sai sarki ya aika manzo ya zo wurinsa,", "body": "\"Kasancewa a gaban sarki\" yana nufin kasancewa ɗaya daga cikin bayinsa. AT: \"Sarkin Isra'ila ya aiki ɗaya daga cikin bayinsa a matsayin manzo\" (Duba: figs_idiom)" }, { "title": "amma da manzon ya zo wurin Elisha, sai ya ce da dattawan", "body": "Anan Elisha yana magana da dattawan tun kafin manzan sarki ya iso. AT: \"lokacin da manzon ya kusan isa, sai Elisha ya ce wa dattawan\" (Duba: figs_explicit)" }, { "title": "Dubi yadda wannan ɗan mai kisan kai ya aika a sare mani kai?", "body": "Elisha ya yi amfani da wannan tambaya don ya jawo hankali ga manzannin da kuma zagi sarki. Ana iya rubuta wannan azaman sanarwa. AT: \"Duba, wannan ɗan mai kisan kai ya aiko wani ya cire mini kai!\" (Duba: figs_rquestion)" }, { "title": "ɗan mai kisan", "body": "Wannan yana nuna cewa sarkin Isra'ila yana da halayen mai kisan kai. AT: \"wannan mutumin da ya yi kama da mai kisan kai\" ko \"wannan mai\nkisan kai\" (Duba: figs_idiom)" }, { "title": "ya aiko", "body": "An fahimci cewa ya aiko da mutum. AT: \"ya aika wani zuwa\" (Duba: figs_ellipsis)" }, { "title": "a ɗauke mani kai", "body": "Wannan yana nufin fille kansa. AT: \"a datse kaina\" ko \"a fille kaina\" (Duba: figs_euphemism)" }, { "title": "Duba, yaushe", "body": "Elisha ya yi amfani da wannan kalma a nan don jawo hankalin dattijon game da abin da ya faɗi. AT: \"Saurari abin da nake so kuyi: yaushe\" " }, { "title": "kulle ƙofar a hana masa shiga", "body": "Idan an kulle kofa ga wani yana nufin yana rufe kuma ba za su shiga ta ciki ba. AT: \"kulle ƙofar don kada ya shiga\" (Duba: figs_idiom)" }, { "title": "Ashe ba ƙarar sawun mai gidansa na biye da shi ba?", "body": "Elisha ya yi amfani da wannan tambaya don tabbatar wa dattawan cewa sarki ba ya zuwa kusa da shi. Wannan tambaya ana iya rubuta ta azaman bayani. AT: \"Sautin ƙafafun maigidansa yana hannun dama.\" ko kuma \"Sarki zai zo da wuri bayan ya dawo.\" (Duba: figs_rquestion)" }, { "title": "ga shi, ɗan saƙon", "body": "Kalmar \"ga shi\" tana faɗakar da mu game da isowar manzo. " }, { "title": "ɗan saƙon ya sauko ya zo wurinsa", "body": "Dan saƙon ya iso, sarki kuma kamar yadda Elisha ya faɗa zai yi. Kalmomin \"sun\nsauko gare shi\" yana nufin cewa sun isa wurin da yake. AT: \"manzo da sarki sun iso\" (Duba: figs_explicit da figs_idiom)" }, { "title": "duba wannan matsala", "body": "\"Lallai wannan matsala.\" Kalmar \"duba\" a nan yana ƙara ƙarfafawa ga abin da ya biyo baya. Kalmomin \"wannan matsala\" tana nufin yunwar Samariya da wahala da ta haddasa. " }, { "title": "Don me kuma zan ƙara jiran Yahweh?\n", "body": "Wannan sarki yayi amfani da wannan tambaya don nuna cewa bai yi imani da cewa Yahweh zai taimake su ba. Ana iya rubuta wannan azaman sanarwa. AT: \"Don me zan ci gaba da jiran Yahweh ya taimake mu?\" ko kuma \"Ba zan ƙara jiran taimako daga wurin Yahweh ba! (Duba: figs_explicit da figs_rquestion)" } ]