[ { "title": "Ko babu wani annabin Yahweh ne, da zamu tambayi Yahweh ta wurinsa?", "body": "Yehoshafat ya yi amfani da tambayar don nuna cewa ya tabbata cewa akwai annabi a can da kuma gano inda yake. Ana iya rubuta wannan azaman sanarwa. AT: \"Tabbas akwai wani annabin Yahweh a nan! Ku faɗa mini inda ya dace, saboda haka za mu iya neman Yahweh ta wurinsa.\" (Duba: figs_rquestion)" }, { "title": "Shafat", "body": "Wannan sunan mutum ne. (Duba: translate_names)" }, { "title": "shi ne ya zuba ruwa a hannun Iliya", "body": "Wannan ma’anar yana nufin cewa shi mataimakan Iliya ne. Bayanin “zuba ruwa\na hannu” kwatankwacin ɗaya daga cikin hanyoyin da ya bauta wa Iliya. AT: \"wanda ya kasance mataimaki ga Iliya\" (Duba: figs_idiom)" }, { "title": "Maganar Yahweh na tare da shi", "body": "Wannan yana nufin cewa shi annabi ne kuma Yahweh yana faɗa masa abin da zai faɗa. AT: \"Yana magana da abin da Yahweh ya ce masa ya\nfaɗi\" (Duba: figs_explicit)" }, { "title": "suka tafi wurinsa.", "body": "Sun tafi su ga Elisha kuma sun yi shawara da shi game da abin da ya kamata su yi. Cikakken ma'anar wannan bayanin ana iya bayyana shi sarai. AT: \"ya je ya ga Elisha don tambayarsa abin da ya kamata su yi\" (Duba: figs_explicit)" } ]